Gwmnatin tarayyar Najeriya ta ce rukunin farko da rigakafin cutar Korona zai iso ƙasar nan da ƙarshen watan Janairun da muke ciki.
Babban sakatare a ma’aikatar lafiya matakin farko a Najeriya Dakta Shu’aib Faisal ne ya bayyana hakan a yayin da suke shirye shiryen gyara gurbin da za a ajiye rigakafin wanda gwamnatin ta tanada.
Adadin rigakafin da zai iso za a yiwa mutane dubu hamsin a Najeriya wanda ya haɗa da gwamnoni, shugabannin addini, da shugabannin gargajiya, sai ma’aikatan lafiya da sauransu.
Dakta Shu’aib ya ce da zarar rigakafin ya iso za a bawa ma’aikatar hukumar lura da abinci ta ƙasa NAFDAC don tabbatar da ingancinsa.
A don haka ya buƙaci al’ummar Najeriya su ce tsoro kuma su kwantar da hankalinsu a kan rigakafin.
Sannan ya ce nan da wani lokaci ƙanƙani za a fara samar da rigakafin cutar a nan gida Najeriya duka dai domin daƙile yaɗuwar cutar a ƙasa baki ɗaya.