Rundunar yan sanda ta tabbatar da mutuwar wani matashi da ya hallaka kansa ta hanyar rataye kansa da wutar lantarki.

Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige ne ya bayyanawa Mujalar Matashiya hakan ta wayar tarho.
Ya ce matashin ya hallaka kansa ne tun a daren Alhamis ɗin da ta gabata zuwa wayewar jiya Juma’a, sai dai har yanzu bas u gano dalilin da ya sa matashin yahallaka kansa ba.

Ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike ta hanyar ƴan uwansa, da kuma kiran wayar da yayi na ƙarshe.

Matashin mai shekaru 22 a duniya, ya kashe kansa ne a yankin Aboro na ƙaramar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.