Hukumar shige da fice a Najeriya ta tabbatar da sace kakakin hukumar ta jihar Edo.
Ƴan bindiga sun sace Esene Bridget ne yayin da take kan hanya zuwa coci a jiya Lahadi.
Maharani sun tilasta mata shiga motarsu yayin da suka ban motar tata a a wajen da suka tareta.
Sai dai babu wani rahoton kiran waya daga masu garkuwa da mutanen.
Mai Magana da yawun ƴan sanda a jihar edo Chidi Nwabuzor y ace bashi da hurumin Magana a dangane da lamarin.
Harin ƴan bindiga dai na daɗa ta’azzara musamman ganin yadda ake ƙara samun rahoton yin garkuwa da mutane daban daban, tun daga masu muƙami, masu mulki da jami’an tsaro.