Hukumar kula da kula da ma aikatan ƴan sanda ta amince da ƙarin girma ga manyan ƴan sanda 20,356.

Cikin waɗanda suka samu ƙarin girma akwai Kwaamishinonin ƴan sanda tara da suka samu muƙami zuwa muƙamin mataimakin sufeton ƴan sanda AIG.
Daga cikinsu akwai kwamishinan ƴan sandan Kano Habu Ahmadu Sani.

Sai mataimakan kwamishinan ƴan samda tara suka samu ƙarin girma zuwa Kwamishinonin ƴan sanda.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Ikechukwu Ani ya fitar a yau, ya ce an amince da ƙarin girman ne tun ranar 25 ga watan daa muke ciki.