Babbar kotun jihar Abeokuta ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mai suna Ibrahim Toyin bayan an same shi da aikata fashi.

Alƙaliyar kotun Ayokunle Rotimi-Balogun ce ta yi hukuncin bayan da ta gamsu da dukkan hujjojin da aka gabatarwa kotu.
Ta ce hujjoji sun tabbatarwa da kotu cewar an samu mutumin da aikatawa wata mai suna Margret Sodeke fashi a ranar 25 Agusta 2012.

A yayin fashin kuma ya kwace Jakarta wadda ke ɗauke da kuɗi naira 15,000 da katin cirar kudi sai sauran muhimman abubuwa.

Bayan samun hujjojin da suka tabbatarwa da kotu shi ya aikata laifin, daga ƙarshe an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.