Lauyan da ya jagoranci ɓangaren wadda ake zargi da kashe yar aikin ta Barista Ibrahim Cheɗi ya bayyana wa Mujallar Matashiya cewar suna da kwarin gwiwar gabatar da hujjojin da za su ba ta kariya a gaban shari’a.

A yayin da yake yiwa Mujallar Matashiya ƙarin haske dangane da zaman kotun a yau, ya ce kotun na duba yuwuwar bayar da belin Fatima Hamza daga nan zuwa ranar 16 ga watan da muke ciki.
Barista Cheɗi ya ce akwai dalilai da suka buƙaci a bayar da belin wadda ake zargi na ganin ba ta da lafiya, ga jajririn ciki da ta ke ɗauke da shi sannan ga jaririya da ta ke raino.

Lauyoyin ɓangaren gwamnati da wadda ake zargi sun gabatar da hujjoji a kan wadda ake zargi, sannan alƙalin zai yi nazari a kan yuwuwar bayar da belin ko akasin haka daga yau zuwa ranar 16 ga wata.

A zaman kotun na yau wadda ake tuhuma ta musanta zargin da ake yi mata.
A cewar Barista Cheɗi “Ka san tuhuma ta kisan kai kala-kala ce, akwai wadda ke ƙarƙashin sashe na 221 da ƙarƙashin sashe na 222 da kuma shashe na 224.
“Amma sashen da ake tuhumarta a kai sashe ne da mafi tsananin hukuncin da za a yanke shi ne ɗaurin rai da rai, ko wasu shekaru a gidan gyaran hali, ko kuma a ba da zaɓin tara.
“Kuma yanayin da take ciki ko da a cikin manyan laifukan kisan kai ne kotu na iya bayar da belin wadda ake zargi.
“Idan lokacin gabatar da shaidu ya yi za a sha mamaki saboda yadda mutane suka ɗauki shari’ar ba haka ta ke ba.” a cewar Barista Cheɗi.