Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Rana Ta Biyu Masu Adaidaita Sahu Su Na Yajin Aikin A Kano

An shiga rana ta biyu a yajin aikin da matuƙa babur mai ƙafa uku wanda aka fi sani da adaidaita sahu suka tsunduma a jihar Kano.

Tun a jiya masu tuƙa babur mai ƙafa uku wanda aka fi sani da adaidaita sahu suka fara yajin aiki sakamakon tsarin biyan harajin da wasu daga cikin su suka ƙi aminta da shi.

A sakamakon yajin aikin da masu tuƙa adaidaita sahun suka shiga ya janyo mutane da daman a tattaki a ƙafa wasu kuwa na hawa motocin dakon kaya don biyan buƙatun su.

A safiyar yau kuma gwamnatin jihar Kano ta sanar da samar da sabbin hanyoyin surufi domin rage yawan masu ta’ammali da adaidaita sahu a jihar.

Mai bai wa gwamnan shawara a kan kafafen yada labarai Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan a shafin san a Twitter.

Ya ce gwamnatin jihar ba ta da niyyar haramta sana’ar gaba ɗaya amma za ta samar da hanyoyin da za a sauƙaƙawa al’umma don gudanar da sufuri a jihar.

Mutane na ci gaba da tofa albarkacin bakin su a kai..

A jiya shugaban hukumar Karota Baffa Babba Ɗan’agundi ya jaddada cewar ko da gwamnatin jihar ba dakatar da sana’ar a jihar ba to kuwa za su fito da sabbin tsare tsare daban.

Su kuwa ƙungiyoyiin matƙa adaidaita sahun sun ce ba da yawun su aka tsunduma yajin aikin ba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: