Gamayyar gwamnonin Arewacin Najeriya na gudanar da taro a jihar Kaduna sakamakon taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Gwamnonin tare da shugabannin gargajiya na Arewa suna yin taron ne a gidan Sir Kashim Shettima da ke Kaduna.
A yau Alhamis aka buɗe taron wanda za a mai da hankali a kan matsalar tsaron da ake fuskanta a jihohin arewacin ƙasar.

Ana gudanar da taron ne ƙarƙashin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Haka kuma akwai shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal da ministan yaɗa labarai na ƙasa Lai Muhammad sai sauran masu da riƙe da madafun iko daban daban.
Gwamnonin Arewa sun halarci taron yayin da wasu suka tura mataimakan su don wakiltar su.
Za a yi taron ne tsawon kwana biyu domin shawo kan ɓarkewar al’amuran tsaro a jihohin Arewacin Najeriya.