A yau Asabar aka yi wa shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari allurar rigakafin cutar Korona.

An yi wa shugaban rigakafin ne a yau da misalign ƙarfe 11:52 agogon Najeriya.
Sannan an yi wa mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo allurar kuma aka bas u katin shaidar karɓar rigakafin a nan take.

Shugaba Buhari ya buƙaci ƴan Najeriya su hanzarta zuwa domin a yi musu rigakafin cutar.

A jiya Juma’a aka ƙaddamar da shirin allurar rigakafin wanda aka fara yi wa ma’aikatan lafiya.
Rigakafin ƙarƙashin shirin COVAX za a yi wa kaso 40 na ƴan Najeriya kafin ƙarasowar kasha na biyu da na uku na allurar rigakafin.
A ranar Talata ne aka kawo kashin farko na allurar rigakafin wanda aka tantance ingancin rigakafin a ranakun Laraba da Alhamis sai jiya juma’a aka ƙaddamar da ita ga ma’aikatan lafiya a Najeriya.