Gwamnatin jihar Neja ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun sakandire na gwamnati a jihar har tsawon makwanni biyu.

Biyo bayan fargabar tsaro da ake ci gaba da fuskanta a jihar gwamnatin ta yanke wannan mataki.
Hakan ya biyo bayan wani zama da gwamnatin ta yi da ɓangaren jami’an tsaro daban-daban a jihar.

Kwamishiniyar ilimi a jihar Hajiya Hannatu Jibril Salihu ta ce za a rufe makarantun daga gobe Juma’a 12 ga watan Maris zuwa ranar 26 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Gwamnatin ta sha alwashin shawo kan matsalar tsaron da ake fuskanta, tare d tabbatar da bin dukkan matakin da ya dace don ganin an bai waɗaliban tsaro a mataki daban-daban.
Ko a baya sai da gwamnatin ta yi alƙawarin bai wa jami’an sa kai bindiga domin murƙushe masu satar mutane a jihar Neja.
Jihar Neja na daga cikin jihohin da ƴan bindiga su ka sauya salon satar mutane gama gari zuwa ɗaliban makaranta a jihar.

