Ƙungiyar ɗaliban sharada ta samu tallafin gurabin karatu daga makarantar Ma’ahad Sheikh Uba wanda ya haɗar da Primary, sakadire don gudanar da karatunsu har zuwa lokacin kammala makarantar.

Shugaban Makarantar  Sadiq Sheikh Uba Sharada yace Sunyi hakan ne domin tallafawa marayu da mararsa ƙarfi a kan harkokin ilmi, ya kuma tabbatar da cewa duk ɗalibin da ya samu shiga ɓangaren naziri zai yi karatu har zuwa babbar sakandire.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban Sharada kwamaret Bukhari Isa Sa’id ya nuna farin cikinsa tare da cewar wannan na daga Cikin manyan nasarorin da su ka samu tun bayan kama aiki a ƙungiyar.

Ya kuma ƙara da cewar za su ƙara bibiyar dukkanin makarantun da ke yankin domin sake samarwa sauran marayu gurbi.

A nasu ɓangaren ɗalibai da iyaye sun bayyana farin ikinsu da godiya ga ƙungiyar da makarantar Ma’ahad bisa basu wannan tallafi ba tare da biyan ko sisi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: