Aƙalla mutane 19 ne su ka mutu a sanadin wani hatsari da ya faru a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Lamarin ya faru ne a daren jiya Lahadi wayewar yau Litinin tsakanin wata babbar mota ƙirar tirela da wata motar fasinja da ta tashi daga Kano.

Baya ga mutane 19 da su ka mutu an samu wasu mutane 34 waɗanda su ka ji rauni daban-daban.

An kai gawawwakin babban asibitin Doka kamar yadda shugaban hukumar kiyaye afkuwar haɗɗura ta ƙasa shiyyar Kaduna Hafiz Muhammad ya bayyana.

Mutane 16 daga ciki sun mutu a nan take yayin da uku daga ciki su ka mutu bayan an kai su asibiti.

Sai dai hukumar ta alaƙanta hadarin da gudun wuce sa’a kamar yadda ya bayyana.

Tun tuni hukumar kiyayye afkuwar haɗɗura ke bayyana cewar gudun wuce sa a da gangaci na haddasa haɗɗura wanda ke kai wag a rasa rayuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: