Rundunar ƴan sana a jihar Katsina ta kama wasu mutane uku da ake zargi suna aikata damfara.

Mutanen uku da suka haɗa da Abba Ibrahim, Abdulra’uf Ilyasu, da Usman Adamu sun a sauya murya ne sannan su yi iƙirarin su aljanu ne sun a damfarar mutane.
Dubun su ta cika ne yayin da su ka kira wata mai suna Jamila Sulaiman sannan su ka yi mata barazanatr cutar da iyayenta da ƴaƴan ta matuƙar bata biya kuɗi naira dubu 150 ba.

Matar ta kai wasu kuɗin kamar yadda su ka buƙata sai kuma sauran dubu 97 da ta tura musu ta hanyar banki.

Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi bayan gudanar da bincike a kan su.
Mai Magana da yawun ƴan sandan jihjar SP Gambo Isah ya ce mutanen ana zargin su da aikata laifi makamancin wannan a baya, kuma sun a fakewa da su aljanu ne sais u damfari mutane.
A cewar kakakin za su gurfanar da su a gaban kotu da zarar sun kammala bincike.