Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci manyan hafsoshin tsaron ƙasar da su kawo ƙarshen masu satar mutane da wadanda ke ɗaukar nauyin su.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan al’amuran tsaro a Najeriya Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya ne ya bayyana hakan a yayin ganawar sa da da manyan hafsoshin tsaron.

Ya ce shugaba Buhari ba zai ci gaba da lamuntar ayyukan ƴan bindiga a ƙasar ba.

Ya ƙara da cewa shugaban ya jaddada batun haramta haƙar ma’adanai da tashin jirage a yankin zamfara.

Sannan ya ƙara jaddada batun satar mutane a ƙasar da cewar ba abu ne da gwamnatin sa za ta lamunta ba.

Taron da aka gudanar a yau ya mayar da hankali  a kan al’amuran da su ka shafi tsaro a Najeriya sannan wata hanya ce da za ta nuna wa manyan hafsoshhin dalilin da ya sa aka naɗa su da kuma aikin da ake tsammanin gani daga gare su.

Batun satar mutane a Najeriya abu ne da ya zama ruwan dare musamman yadda ya karaɗe jihohin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: