Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da ƙungiyar IPOB masu rajin kafa ƙasar BIAFRA su ka kai a jiya.

A cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun fadar shugaban ƙasar Mallam Garba Shehu ya fitar, y ace wannan abin takaici ne kuma ta’addanci ne tsagwaron sa.
Shugaba Buhari ya bayar da umarnin jibge isassun jami’an tsaro a jihar Imo domin tabbatar da zaman lafiya.

Haka kuma shugaban ya bayar da umarnin hukunta duk wani da aka samu da hannu a cikin kitsa ta’addancin

Sannan shugaba Buhari ya buƙaci al’umma da su bayar da hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A na zargin masu ƙoƙarin kafa ƙasar BIAFRA da kai harin wanda aka kuɓutar da mazauna gidan yari sama da dubu biyu sannan a ka ƙona helkwatar ƴan sandan jihar.