Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

An Cafke Mutumin Da Ya Shafe Shekaru Biyar Ya Na Yi Wa Ƴar Cikin Sa Fyaɗe

Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta kama wani mai suna Ubong Williams wanda ake zargi da yi wa ƴan cikin sa mai shekaru 12 fyaɗe.

Mutumin mai shekaru 49 a duniya, ya shiga komar hukuma ne bayan wani da ya kai rahoton abinda ya faru zuwa wani caji ofis ɗin ƴan sanda a jihae.

A bayanan da ƴan sanda su ka samu sun ce mutumin ya kasance ya nay i wa yar tasa fyaɗe ne tun ta na shekaru bakwai a duniya.

Mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Abinbola Oyeyemi  y ace sun kama wanda ake zargi a ranar Litinin.

Wanda ake zargin ya bayyana cewar yay i hakan ne sakamakon matar sa ta tsufa sannan ba ta birge shi.

Tuni kwamishinan ƴan sandan jihar ya miƙa ƙorafin zuwa ga helkwatar ƴan sanda da ke Ota domin fadaɗa bincike.

Sannan ya bayar da umarnin kai yarinyar zuwa babban asibiti domin duba lafiyar ta.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: