Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

An Kafa Kwamitin Sauraron ƙorafin Al’umma A Kan Yan Sanda

Ministan yan sanda a Najeriya Muhammad Ɗingyadi ya kafa kwamiti musamman domin duba ƙorafe-ƙorafen al’umma a kan ƴan sanda.

Ministan ya ƙaddamar da kwamitin ne a jiya Laraba a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce an kafa kwamitin ne domin duba ƙorafin ƴan Najeriya a kan ƴan sanda tare da hukunta wadanda su ka yi ba dai-dai ba.

Tun a baya akwai kwamitin wanda ake kira da PPCC sai dai bay a aiki yaddaya kamata saboda rashin kuɗaɗen gudanarwar sa.

Samar da kwamitin zai taimaka wajen bai wa ƴan Najeriya dama domin kwatar musu haƙƙin su daga jami’an ƴan sandan da su ka ci zarafin mutane.

Ministan ya ce abinda ya faru a baya na rikicin rushe rundunar ƴan sanda na SARS, ya faru ne a sanadin rashin aikin kwamitin.

Sannan ya buƙaci kwamitin da ya buɗe dukkan ƙofofin sa domin sauraron al’umma tare da ƙarfafa musu gwiwa a kan cewar za a yi aiki domin kwato musu haƙƙoƙin su.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: