Ma’aikatar hajji da umara a ƙasar saudiyya ta saka doka a kan maus shiga masallacin makkah da madina.

Ma’aikatar ta ce babu wanda zai shiga ,masallacin har sai an tabbatar an yi masa rigakafin cutar Korona.

A cikin shirye-shiryen tinkarar ibada a watan azumi, ma’aikatar ta samar da wata manhaja musamman domin tantance mutanen da aka yi wa rigakafin cutar.

Daga cikin dokokin an haramta wa yara shiga ko kusantar masallatan makkah da madina.

Haka kuma an taƙaita lokutan sallan tuhajjud da tarawih wanda aka ƙayyade mintuna talatin kacal a sallolin biyu a dukkanin masallatan.

Sai kuma tarar riyal dubu goma ga duk wanda ya karya ƙa’idar da aka shimfida wajen gudanar da ibada a masallacin, haka kuma ga duk wanda ya shiga masallacin ba tare da izni ba zai biya tarar riyal dubu ɗaya.

Ko a baya sai da yariman saudiyya salman ya bayar da umarnin rage raka’o’in sallar tuhajjud da tarawih domin kaucewa yaduwar cutar Korona.

A na sa ran za a fara gudanar da azumi a bata daga gobe Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: