Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta kama wasu mata guda biyu da ake zargi da kashe wani mai suna Osita Anwuwanwu.
An kashe mutumin mai shekaru 64 a duniya.
Mai magan da yawun ƴan sandan jihar Legas Muyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi.
Ya ce sun sami ƙorafin ne daga ƴan wanda yam utu sakamakon musu da ya kaure tsakaninsa da waɗanda ake zargi.
Al’amarin da ya saka aka tashi dakarun ƴan sandan domin ziyartar wajen, yayin da su ka je sun tarar da mutumin kwance a ƙasar.
Bayan samun tabbacin mutuwar mutumin, rundunar ta kama mata guda biyu da ake zargi d kisan kuma tuni kwamishinan ƴan sandna jihar ya bayar da umarnin miƙa ƙorafin zuwa babban sashen bincike na rundunar.
Bayan kammala bincike kuma, za a miƙa wadanda ake zargi zuwa gaban kotu domin a yanke musu hukunci.