Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da gwamnonin arewacin ƙasar a yau Alhamis.

An shiga ganawar ne a yau a fadar shugaban da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Daga cikin mutanen da su ka halarci ganawar har da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Farfesa Ibrahim Gambari, sai shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa Simon Lalong.

Sai dai ba a bayyana dalilin shiga ganawar ba har lokacin da muke kammala wannan labara.

Ana zargin zaman nasu zai mayar da hankali ne a kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a mafi yawa daga jihohin Arewa.

A wani labarin kuma gwamnan jihar Za,mfara Muhammad Bello Matawalle yay i wata tattaunawa da shugaban sojin ƙasa a Najeriya.

Gwamnan ya halarci helkwatar sojin da ke Abuja, sai dai bas u bayyana abinda su ka tattauna ba har lokacin da muke kammala wannan labara.

Sai dai ana zargin tattaunawar ba za ta rasa nasaba da hare-haren kiasan gilla da aka yi wa wasu mutane masu yawa a jihar Zamfara ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: