Aƙalla sojoji 18 mayaƙan Boko Haram su ka kashe yayin da su ka kai hari sansanin su da ke jihar Borno a ranar Lahadi.
Rundunar sojin ta tabbatar da mutuwar mutanen sai dai ta ce sojojin da aka kashe guda bakwi ne kacal kuma an kashe su ne yayin da su ke ƙoƙarin daƙile harin da aka kai musu a sansanin su.
Baya ga sojojin da aka hallaka, akwai wasu guda 43 waɗanda su ka ji munanan rauni sai kuma wasu sojoji 50 da su ka ɓata.
A sakamakon harin da mayaƙan su ka kai sansanin sojin a Moinok ƴan Boko Haram sun tafi da makaman sojojin masu yawa sannan su ka ƙone sauran kayayyakin sojojin.
Daga cikin sojojin da su ka rasa ran su har da babban kwamandan rundunar a sansanin.
Harin Moinok na zuwa ne bayan da mayaƙan Boko Haram su ka ci ƙarfin GARIN Geidam Na jihar Yobe.
A ƴan kwanakin nan mayaƙan Boko Haram na tsananta kai hare-hare wanda har ta kai da yawa daga cikin mutanen na barin muhallin su.