Ƴan majalisar dattijai a Najeriya sun yi ganawar sirri da shugabannin tsaro a ƙasar.

Shugabannin tsaro sun shiga ganawar sirrin bayan gayyatar da majalisar ta yi musu a bisa sanar da su halin tsaron da ƙasar ke ciki.

A safiyar yau su ka shiga ganawar sirrin da misalign ƙarfe 11 da miniti 21 na safe kamar yadda BBC su ka ruwaito.

Babban hafsan sojin Najeriya Manjo Janar  Leo Irabo ne ya jagoranci hafsoshin tsaron ƙasar don zuwa majalisar a yau.

Daga cikin waɗanda su ka halarci zaman akwai shugaban hukumar ƴan sandan farin kaya wato DSS da shugaban tattara bayanan sirri ta NIA.

Shugaban majalisar Ahmad Lawal ne ya tarbe su daga bnisani kuma su ka shiga ganwar.

Har lokacin da muke tattara labaran mu ba mu ji batu ko matakin da aka ɗauka bayan tattaunawar ba.

Tun a ranar Talata majalisar ta sanar da cewar ta gayyaci manyan hafsoshin tsaron ƙasar don yi mata bayani a bisa halin da tsaron ƙasar ke ciki.

A wani labarin kuma wakilai a majalisar dattawa na cikin fargaba bayan samun rahoton ƙungiyar Boko Haram za ta kai musu hari.

Jaridar Punch ta tabbatar da cewar ta sami tabbacin hakan daga wasu daga cikin wakilai a zauren majalisar.

Rahoton da su ka samu wanda aka wallafa a ranar 4 ga watan da muke ciki, ya tabbatar da cewar akwai yuwuwar kai hari wasu muhimman wurare a zauren majalisar wanda ake zargin mayaƙan Boko haram da kitsawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: