Hakan ya biyo bayan ci gaba da samun rarrabuwar kai a tsarin tafiyar kwankwasiyya ƙarƙashin jagoranta na ƙasa Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Wani zargi mai ƙarfi da ke nuni da ficewar jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a bisa shirin ficewarsa daga jam’iyyar PDP sakamakon rikicin cikin gida da wasu ke neman yi masa farraƙu.
Rikicin ya samo asali ne sanadin gabatowar zaɓen 2023 wanda ake zargin waɗansu na yin zagon ƙasa a tafiyar tare da ƙoƙarin ƙin bin umarnin sa a bisa wanda ya nuna domin yin takarar gwamna a Kano.

Daga cikin mutanen da ake zargi da cin dunduniyar tafiyar har da jigo a cikin ta Dakta Yunusa Adamu Ɗangwani wanda ke shirin samarwa kansa mafita a shekara ta 2023.

An yi zargin wasu da yin farraƙu a tsagen Kwankwasiyya sanadin tsarin madugun na tsayar da ƴan takara wanda wasu ke ganin ba za su laminci haka a shekara ta 2023 ba.
Duka wannan zargi ya ɓulla a fili ne yayin da wani cikin masu riƙe da madafun iko a tsarin tafiyar ke raba wa magoya bayansa kayan abinci don rage raɗaɗi a watan azumi na bana.
Wani bidiyo da ke yawo ya nuna yadda guda cikin tsarin tafiyar ke yin wasu kalamai da ke kama da raddi a bisa wancen tallafi da ɗaya daga cikin ƴaƴan tsagen kwankwasiyya ke yi.
Yana mai cewar ba za su yarda da wani ɗan takara ba illa tsohon ɗan takarar gwamna a tsagen jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusif.
A gefe guda kuwa wasu na sukar lamarin tare da ganin an tauye musu damar gwada kwanjinsu musamman a yayin zaben da ke gabatowa na shekarar 2023.
Wannan rikici ya sha faruwa wanda hakan ya sa wasu su ka bar tsarin tafiyar tsare da komawa tafiyar APC ƙarƙashin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a shekarar 2019.
Kafin haka dama akwai tsohon rikici a jam’iyyar PDP tsakanain ƴan kwankwasiyya da ƴan tsohuwar jam’iyyar PDP wanda a baya ya dawo suke ganin ya na musu ƙarfa-ƙarfa.