Ministan babban birnin tarayya Abuja Muhammad Bello ya bayar da umarnin taƙaita mutane yayin gudanar da sallar idi a Abuja.

Ministan ya dakatar da gudanar da idin ƙaramar sallar a babban masallacin idi na ƙas da ke babban hanyar Umaru Musa Ƴa’adua a Abuja.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran minitan Mista Anthony Ogunlaye ya fitar, ya ce an umarci mutane a su gudanar da sallar idin su a masallatan juma’a mafi kusa da su.

An yanke hukuncin hakan ne bayan wani zama tsakanin mistan da wakilan malamai a Abuja.

Umarnin yin sallar idi a masallatan juma’a wanda aka ce kada a haura mutane hamsin a masallaci.

Sanarwar ta umarci mazuna Abuja da su gudanar da shagulgulan sallar su a gidajen su, yayin da ak abayar da umarnin rufe dukkanin gidajen wasa, da sauran wuraren shaƙatawa.

Dukkan wannan mataki ya biyo bayan saka sabuwar dokar kulle da aka yi a Najeriya domin rage yaɗuwar cutar Korona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: