Aƙalla sama da mutane dubu 300 cutar Korona ta hallaka a ƙasar Indiya a yayin da zagaye na biyu na cutar ke ƙara shiga wasu ƙasashen duniya.

A yau Litinin hukumomi a ƙasar su ka bayar da sanarwar mutanen da su ka mutu sun kai sama da dubu 300.

Bayan samun ƙarin mutuwar mutane 4,453 adadin mutanen da su ka mutu sun kai 303,720.

Hukumomi a ƙasar sun bayyana dalilin ƙara yaɗuwar cutar, wanda su k ace cutar ta shiga wasu ƙauyukan jihohin lamarin da ya sa adadin masu kamuwa da ita su ka ƙaru har ta ke kashe wasu daga ciki.

A cewar hukumomin, cutar ta shiga ƙauyukan da su ke da ƙarancin ilimin yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar.

Ƙasar Indiya ta kasance ƙasa ta uku da cutar Korona ta fi yi wa ta’adi bayan a yayin da cutar ta sake zagayowa a karo na biyu.

Idan ba a manta ba, ƙasar Indiya ta samar da rigakafin cutar Korona na Astra Zeneca wanda aka rarraba a ƙasashen Afrika ƙarƙshin shirin Covax don rage yaɗuwar cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: