Gwamnatin jihar Kano ta haramta shan taba sigari a cikin jama’a.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta AMinu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a yayin taron yaƙi da shan taba sigari a cikin al’umma.

Wannan wani mataki ne da aka ɗauka domin rage yawan masu mutuwa a sanadin shan taba sigari.

Akwai ,ƙiyasin mutane 16,100 waɗanda ke mutuwa a sanadin shan taba sigari a Najeriya.

Haka zalika gwamnatin ta haramta siyar da taba sigari ga ƙananan yara waɗanda ke ƙasa da shekaru 18 a duniya.

Dakta Tsanyawa y ace za su haɗa hannu da dukkanin masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dokar da aka saka a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: