Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ne ya bayyana hakan yayin da ya ziyarci helkwatar soji da ke Abuja.

Ganduje ya ce ƴan bindiga na taruwa a dajin falgore, babban daji da ya hada iyaka da jihohin ƙasar.
Gwamnan ya yi ta’aziyyar marigari tsohon hafsan sojin ƙasan Najeriya tare da roƙon sabon hafsan sojin da ya ziyarci dajin don duba yuwuwar ci gaba da aikin kafa sansanin soji a cikin dajin.

Babban hafsan sojin ƙasa Janar Farouƙ Yahaya ya sha alwashin ziyartar dajin falgore tare da nemo hanyar da za a magance ta’addancin da ake a cikin sa.
