An rabawa jami’an tsaro kekuna guda 30 sai motoci guda 89 sannan baburan hawa guda 283 sai adaidaita sahu guda 4.

Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da sace ɗaliban islamiyya 136  wanda ƴan bindiga su ka yi a ƙarshen makon da ya wuce.

Mataimakin gwamnan jihar Ahmed Ketso ne ya tabbatar da hakan yayin da yake bayani a dangane da lamarin a babban birnin jihar Neja wato Minna.

Ya ce gwamnatin jihar ta tanadi isassun jami’an tsaro waɗanda za su yi aikin ceto ɗaliban.

Sannan an raba ababen hawa ga jami’an waɗanda za su yi aiki domin ceto ɗaliban da aka sace.

An raba babura guda 283 da motoci guda 89 sai adaidaita sahu guda huɗu da kuma kekuna guda 30 ga jami’an tsaron ga dakarun tsaro na ɓangare daban-daban domin ceto ɗaliban da aka sace.

Daga cikin waɗanda aka bai wa ababen hawan har da jami’an sa kai na Bijilanti.

Ƴan bindiga sun shiga makarantar islamiyya ta Tagina a jihar Neja tare da sace ɗalibai maza da mata a ciki.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: