Hukumar lafiya ta duniya WHO ta tabbatar ta ingancin rigakafin cutar Korna ta Sinovac-CoronaVac wanda ƙasar China ta samar.
A ciki wata sanarwa da hukumar ta fiytar ta ce rigakafin na da ingancin da za a iya amfani da ita a ƙasashen duniya.
Hukumar ta ce har yanzu akwai buƙatar ƙarin rigakafin cutar domin ganin an rage yaɗuwarta a faɗin duniya.
Tuni aka fara amfani da rigakafin Astra Zeneca wanda ƙasar indiya ta samar a tun da farko,
Hukumar ta bayar da umarnin fara amfani da rigakafin na Sinovac-CoronaVac a ƙasashen duniya.
Ɓullar cutar Korona ya dakatar da gudanarwar al’amura a ƙasashen duniya.
Ƙasashe daban-daban na dakatar da shiga ƙasar muddin ba a yiwa mutum allurar rigakafin cutar Korona ba.
Wannan wani mataki ne da ake ɗauka domin shawo kan annobar tare da ƙoƙarin daƙile yaduwarta a cikin al’umma.