Gwamnatin Najeriya ta baiwa hukumar lura da kafafen yaɗa labarai umarnin fara shirin samar da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na Intanet.

Ministan yaɗa labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan yayin bayani a kan rufe shafin sada zumunta na Tuwita a ƙasar.
Ministan ya ce shafin na taka rawa wajen raba kan ƴan Najeriya.

Sannan ya bayyana cewar sun baiwa hukumar lura da kafafen yaɗa labarai domin duba tsarin bayar da lasisi ga kafafen yaɗa labarai na intanet.

Rufe shafin tuwita dai ya janyo cece-kuce daga ƴan Najeriya.
Gwamnatin Najeriya na zargin kamfanin tuwita da goyon bayan masu tada ƙayar baya a kudu maso gabashin Najeriya wajen ci gaba da goyon bayan ayyukan su.