Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar gaggawa da manyan hafsoshin tsaron ƙasar.

An yi ganawar ne a yau a fadarsa da ke Abuja.

Manyan hafsoshin tsaron Najeriya sun halarci ganawar ciki har da sabon harsan sojin ƙasan Najeriya Farouƙ Yahaya.

Wannan ne taron tsaro na farko da sabon hafsan sojin ƙasan ya halarta tun bayan naɗa shi a matsayin hafsan sojin ƙasan ƙasar.

Daga cikin wadanda su ka halarci ganawar akwai mataimakin shugaban ƙasa farfesa Yemi Osibanjo, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha sai Babagana Munguno mai bai wa shugaban ƙasa shawara a kan al’amuran tsaro.

Sai dai ba a bayyana abin da shugabannin su ka tattana ba.

Har yanzu majalisar dattawan ƙasar ba ta tabbatar da sabon hafsan tsaron ƙasan Najeriya ba, wanda aka nada shji bayan mutuwar marigayi Janar Ibrahim Attahiru wanda ya rasu a hatsarin jirgi a Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: