Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya karɓi rahoton da wani kwamiti ya tattara a kan matsalar satar mutane a jihar.

A cikin rahoton da kwamitin ya gabatar ƙarƙashin tsohon sufeton yan sanda Muhammad Abubakar, kwamitin ya gano cewar mata 4,983 aka kashe wa mazajen su kuma aka bar su da marayu 25,050.
Sannan mutane 190,340 sun rabu da muhallin su a sanadin tashe-tashen hankulan da aka fuskanta a jihar Zamfara.

Haka kuma rahoton ya gabatar da cewar an sace mutane 3,672 yayin da aka karbi kudin fansa naira biliyan uku.

Sannan an sace babura da motoci guda 147,800 sai akuyoyi da tinkiyoyi guda 141 sannan shanu guda 2,015 sai jakuna da raƙuma guda 2,600.
Dukkanin wannan rahoto rikici ne da ya faru daga watan Yuni na shekara ta 2011 zuwa 29 ga watan mayun shekarar 2019.
Bayan an gabatar masa da rahoton ya fara duba hanyoyin da za a bi domin magance al’amarin satar mutane da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar.