Wasu mafarauta a jihar Kogi sun kama ƴan bindiga huɗu a maɓoyarsu da ke cikin daji.

Mafarautan sun kama ƴan bindigan ne a wani daji da ke ƙaramar hukumar Okehi ta jihar Kogi.
Yayin da mafarautan su ka cimma ƴan bindigan sun lalata tabar wiwi mai yawa wanda ake zargi ta ƴan bindigan ce.

Ƴan bindigan suna amfani da wani ɓangare a cikin dajin wajen noman tabar wiwi tare da amfani da wasu karnuka don yin gadin wajen.

A yayin da mafarautan su ka shiga dajin an kashe wasu daga cikin karnukan da dama.
Shugaban ƙaramar hukumar Okehi Abdukraheem Ohiare ya tabbatar da cewar jihar Kogi ba za ta lamunci ayyukan ta’addanci ba sannan za su ci gaba da farautar mutanen da ke aikata ta’addanci a ko ina su ke a faɗin jihar.