Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya musanta labarin da aka yin a cewar wasu yan bindiga na kafa sansani a dajin falgore.

Gwamnan ya miusanta wannan labara ne a yayin wata hira da BBC su ka yi da shi.

Ya ce sam bah aka yake nufi a maganar sa ba, abin da yake nufi shii ne fargabar yaduwar yan bindiga a wasu dazukan Najeriya bayan tarwatsa su a jihohin da su ke.

A don haka ne ma ya buƙasci shugaban Najeiya Muhammadu Buhari da ya samar da sansanin horas da sojoji a dajin.

Ya ƙara da cewa idan har akwai dajin da ƴan bindiga za su iya ɓuya a Kano bai wuce dajin Falgore ba a don haka ya buƙaci yi wa tifkar hancin tun kafin hakan ta fariu.

Gwamna Ganuje ya ce sam babu ƴan bindiga d suka kafa sansani a dajin Falgore sannan ya na iya ƙoƙarin sa wjen ganin sun haɗa kai da sauran gwamnonin jihohi dpomin magance matsalar tsaro.

Tuni aka fara horas da ƙanana sojoji aikin harbi a dajin Falgore bayan kashe kuɗi wajen gine-gine a dajin kamar yadda gwamnan ya bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: