Shugaban Najriya Muhammadu Buhari ya hori sojin ƙasar da su sake zage damtse wajen yaƙara yyukan ta’addanci a ƙasar.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi yau a Maiduguri babban birnin jihar Borno yayin da ya ziyarci sansnain rundunar tsaron ta hadin gwiwa da ke maimalari a jihar Borno.

Shugaban ya sake jaddadawa cewar akwai aiki mai girma a gaban rundunar sojin don ganin sun magance matsalar tsaron da ake fuskanta.

Ya ƙara d acewa wajibi ne su magance matsalar domin ƙalubale ne a garesu don ganin an kawar da duk wani aikin ta’addanci a ƙasar.

Shugaba Buhari ya jinjinawa jami’an a bisa ƙoƙarinsu tare da jan hankalinsu wajen ganin an magance matsalar tsaro a arewa maso gashin ƙasar da sauran ƙasa baki ɗaya.

A yayin da yake jawabin godiya shugaban rundunar hadin kai Manjo Janar F.O Omogwui ya yaba ga ziyarar shugaban tare da nanata cewar wannan zai zamto musu ɗamba ta sake ɗaura ɗamarar yaƙi da ta’addanci a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: