Wasu mutane a birnin tarayyar Najeriya wato Abuja sun gudanar da zanga-zanga a Titin Umaru MuSA Y’r’adua a yau.

Mutanen ɗauke da kwalaye masu rubutun buƙatar shugaban ƙasa ya sauka daga mulki, sun cinna wuta a kan titin.

Masu zanga-zangar sun cinna wutar ne a tskiyar titi lamarin da ya sanya masu ababen hawa tafiya a sannu sannu.

Ana zargin mutanen sun fito ne daga jihohin kudancin Najeriya.

An fara gudanar da zanga-zanga tun a ranar 12 ga watan da muke ciki wadda aka ware a matsayin ranar Dimokaraɗiyya a Najeriya.

Jihohin daban-daban sun yi zanga-zangar nuna ƙin goyon bayan mulkin shugaba Buhari ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Har lokacin da muke kammala labarain ba mu samu rahoton hatsaniya ko makamancin haka ba sakamakon zanga-zangar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: