Connect with us

Labarai

Za Mu Ci Gaba Da aikin Titin Goron Dutse Zuwa Jakara – Ganduje

Published

on

 

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin kammala titin nan da ya taho daga Jakara zuwa Gorondutse ba da jimawa ba.

Har ma a nan take ya ba da umarni ga Kwamishinan Ayyuka da ya yi gaggawar bin takardun aikin, dan ganin a ina a ka kwana kuma a ina za a tashi.

Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke kaddamar da Makon Shirin Tsaftace Birnin Kano, wanda a ka kaddamar a katafariyar kwatar nan ta Jakara, wacce ta zarce har zuwa Kwakwaci, gaban Gidan Jarida na Triumph, yau Talata.

Titin wanda tsohuwar gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ta fara kuma ta watsar ya dade ya na ci wa mutanen yankin tuwo a kwarya.

Daidai lokacin da Gwamna Ganduje ya yi wannan maganar kammala aikin titin sai wajen ya dau wata irin sowa daga daruruwan mutanen da su ka je wajen waccan kaddamarwa.

Ya ce “Mun biyo ta wannan titi mai muhimmanci mun ga yadda aikinsa ya kasance. Yanzu haka ina tare da Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, na kuma ba shi umarnin da ya koma ofis ya dauko fayil din a ga yadda aikin yake, saboda a yi gaggawar kammala aikin.”

“Wannan titi mai muhimmanci, na Sheikh Mahmud Salga, da ya faro daga kan titin Malam Aminu Kano, Gorondutse, zuwa Jakara bola, za mu tabbatar an kammala shi ba da jimawa ba,” in ji shi.

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Talata, 22 ga Watan Yuni, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatina Ta Yi Duk Abinda Ya Dace Ga Ƴan Najeriya – Buhari

Published

on

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tabbatar da cewar gwamnatinsa ta yi duk abinda ya dace wajen ciyar da Najeriya gaba.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka a cikin jawabinsa na zagayowar ranar samun ƴancin kai a Najeriya.

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta yi ƙoƙari matuƙa wajen bunƙasa tattalin arziƙi da kuma tantance bayanai a kan asusun ajiyar banki ta ƴan ƙasar.

Haka kuma ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankalin wajen bunƙasa aikin gona wanda hakan ya zamtowar ƙasar hanyar nasara duka a ƙarƙashin mulkinsa.

Shugaba Buhari ya ce ya na jin matuƙar ciwo a bisa yajin aikin da ƙungiyar Malamn jami’a su ka shafe fiye da watanni bakwai su na yi.

A ɓangaren yajin aikin, ya ce gwamnatinsa ta yi tsare-tsare da aka shafe fiye da shekaru 11 ba a yi su a a gwamnatocin baya.

Shugaban ya sake tabbatar da aniyarsa na ganin an gudanar da sahihin zaɓe a shekarar 2023.

Wannan ne karo na ƙarshe da shugaban ya yi jawabin tunawa da zagayowar ranar samun ƴancin kai a matsayinsa na shugaban ƙasa.

Continue Reading

Labarai

Ganduje Ya Buƙaci Matasa Su Rungumi Zaman Lafiya

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci al’ummar jihar su zamto jakadun zaman lafiya.

Gwamna Ganduje ya bayyana buƙatar hakan a cikin jawabinsa na zagayowar ranar samun ƴancin kai da ya gabatar a filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar Ƙofar Mata a Kano.

Yayin da Najeriya ke cika shekaru 62 da samun yancin kai, gwamna Ganduje buƙaci jama’a su kauceea dukkan maganganu da ayyukan da za su iya rusa zaman lafiya a jihar Kano.

Gwamnan ya godewa mutanen Kano a bisa haɗin kai da su ka bayar tare da tabbatar musu da cewar a shekara mai zuwa wani gwamnan ne zai kasance a Kano ba shi ba.

Sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da haƙuri a kan kasancewar bambancin ɗabi’u addini da al’ada wanda jihar Kano da Najeriya ke da su.

A taron da aka gudanar, sarkin Kano Alhaji aminu Ado Bayero ya jagoranci addu’a ta musamman a kan zaman lafiya tare da buƙatar matasa da su zamto jakadun zaman lafiya a duk wajen da su ka sami kansu.

Continue Reading

Labarai

Sarkin Kano Ya Buƙaci Matasa Su Kaucewa Fitina Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe

Published

on

An Ja hankalin Matasa da yan Siyasa su gujewa dukkannin abunda zai tada hankalin al’uma a lokutan yakin neman zabe: Sarkin Kano.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yaja Hankalin al’umma da yan siyasa su rika yin kalamai masu inganci a cikin al’umma

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci gudanar da addu’oi na musamman domin samun zaman lafiya ga kasa baki daya wadda aka gudanar a babban masallacin juma’a dake cikin birnin Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya shirya wannan addu’a ne domin yiwa kasa addu’a da kuma zabuka da suke tunkararmu a shekara 2023.

Mai martaba sarkin kazalika yayi kira ga Matasa su gujewa dukkan abinda zai kawo fitina a lokutan yakin neman zabe.

Sarkin ya buƙaci al’umma su zama masu Ladabi da biyayya da tausasa harshinansu.

Kuma sarkin yayi fatan dukkan yan Siyasa zasu karbi shawarwari da Malamai suke bayarwa na suyi yakin neman zabe cikin nutsuwa ba tareda wani tashin hankali ba.

Daga nan kuma Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace shirya adduoin yazo dai dai lokacin da ake bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun yancin kai.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: