Hukumar shirya jarrabawar NECO ta tsawaita kwanakin rijistar ga ɗalibai.

Hakan ya biyo bayan kiraye-kiraye da iyaye su ka yi a bisa takaitaccen lokacin da aka saka na yin rijistar bayan fitowar jarrabawar kwalifayin.
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar ilimi a jihar Kano Aliyu Yusif ya fitar, ya ce gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da ma’aikatar ilimi ne su ka roƙi hukumar ta tsawaita lokacin.

A halin yanzu an tsawaita lokacin zuwa ranar 30 ga watan da muke ciki har ƙarfe 12 na dare.
