Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe gungun mayaƙan Boko Haram ɓangaren Sheƙau da ɓangaren ISWAP jihar Borno.

Sojojin sun kashe mayaƙan ne a yankin Bula a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno da ke gabashin Najeriya.
Sojojin sun kashe mayaƙan ne yayin da su ka nufi dajin sambisa a wasu manyan motocin yaƙi guda shida.

An shafe sama da awanni biyu ana fafatawa tsakanin mayaƙan da rundunar sojin, kuma a nan ne aka kashe jami’an soji guda biyu.

Rundunar ta yi zargin mayaƙan na shirin kai hari ne bayan sun taru sai dai kuma su ka samu nasarar cin musu tare da halaka da yawa daga cikin su.
Sanarwar ta ce mayaƙan da su ka gudu na ɗauke da raunin harbi a jikinsu yayin da aka kashe mafi yawa daga ciki.
A makon da ya wuce ne mayaƙan ISWAP su ka bayar da sanarwar hadewarsu da ƙungiyar Boko Haram ɓangaren Sheƙau domin ci gaba da kai hare-hare.