Ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya sun yi wani zaman tattaunawa tare da cimma matsaya a kan yankin su.

Daga cikin matsayar da s ka cimma akwai fitar da ɗan takara daga yankin su wanda su k ace wajibi ne wanda zai gaji kujerar shugabancin ƙasar Najeriya ya kasance ya fito daga wajen su.
Ƙungiyar ta cimma wannan matsaya ne bayan wata ganawa da su ka yi jiya Litinin a birnin Legas.

Sannan sun cimma matsaya a kan abubuwa kamar haka

Tabbatar da buƙatar samar da yan sanda a kowacce jiha kuma na ƙashin kanta.
Sannan wajibi ne duk wata hukuma idan za ta gudanar da wani aiki na sumame ta sanar da su kafin aiwatarwa.
Haka kuma sun tsayar da ranar 1 ga watan satumba a matsayin ranar da dokar hana kiwo a jihohin su za ta fara aiki.
Haka kuma a zaɓi jihar Legas a matsayin helkwatar ƙungiyar gwamnonin kudancin.