An ɗauki matakin haka ne don hana yaɗuwar cutar Korona.

Gwamnatin Najeriya ta soke bikin hawan salla a ƙasar.
Shugaban kwamitin yaƙi da cutar Korona Boss Mustapha ne ya bayyana haka a yau Lahadi.

An bukaci jihohin Legas Kano da wasu jihohin da ke bikin al’adar hawan sallag da su soke dukkan hawan sallar da aka saba yi a al’adance.

An ɗauki matakin haka ne don hana yaɗuwar cutar Korona da ake fargabar ɓarkewar ta a karo na uku.
Ya ce kwamitin na ci gaba da bin hanyoyin da su ka dace don kare jama’a daga cutar.
Daga cikin dalilan da su ka sa a ka ɗauki wannan mataki akwai shigowar baki daga kasashen ketare wanda aka tabbatar akwai nau’in cutar a kasar.
Tun tuni wasu masarautun a Najeriya su ka soke bikin hawan bisa fargabar tsaro da ake fuskanta.