Bayan buɗe shafin yanar gizo da hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta yi don sauƙaƙa wa a yau 19 ga watan Yuli an fara rijistar katin zaɓen ga mutanen da ba su tura bayanan su ba.

Mutanen da shekarun su ya kai 18 zuwa sama kuma ba su da katin ne za a iya yi wa rijistar, sai waɗanda katin su ya lalace ko ya ɓata ko su ka samu sauyin gari ko unguwa.
Hukumar zaɓe a Najeriya INEC ta fara ɗaukar hotunan yatsun mutanen da su ka aika bayanan su ta wayar tafi da gidan ka.

Ga mutanen da ba su aika bayanan su ba ma za su iya zuwa ofishin hukumar na ƙananan hukumomin su domin bayar da bayanan su.

Har yanzu ƙofa a buɗe ta ke ga mutanen da ke son aika bayanan su ta wayar salula. Hanyar da za a bi ita ce, cvr.inecnigeria.org ko kuma cvr.inec.gov.ng.
Bayan aika bayanan ku za a aiko muku da ranar da za ku je don ɗaukar hotunan yatsun ku.
Hukumar na kira ga jama’a da su hanzarta don yin rijistar katin zaɓen su.
A makon da ya gabata sai da hukumar zaɓe INEC reshen jihar Kano ta koka a bisa yadda mutane ba su mayar da hankali don yin rijistar katin zaɓen ba.