Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatar da buɗe makarantu a jihar ba tare da saka wani lokacin buɗewa ba a nan gaba.

Gwamnan jihar Malam Nasir El’rufa’I ne ya sanar da hakan yau Litin in a taron masu ruwa da tsaki a kan ilimi na jihar.
Gwamna El’rufai ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin samun bayanai a kan tsaron jihar.

Sannan ya gargadi mutanen jihar da su kula domin gwamnatin jihar ta sake aike da jami’an tsaro don yaƙar su.

Sannan gwamnatin za ta ci gaba da kula da daliban jihar daga hare-haren ƴan bindiga, a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare ga ɗalibai da ɗai-ɗaikun mutane a Kaduna.
Gwamnatin Kaduna ta rufe makarantu a jihar ne sakamakon ci gaba da kai hare-hare tare da sace ɗalibai a makarantun jihar.
A halin yanzu akwai ɗalibai da dama da ke hannun yan bindigan waɗanda ke tsare a hannun sub a tare da an kuɓutar da su ba.
Gwamnatin Kaduna ta sha alwashin kawar da ƴan bindigan da su ka addabi jihar ba tare da ta yi sulhu da su ba.