Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewar za ta ɗaukaka ƙara a kan shari’ar da aka yi wa shugaban mazahabar shi’a a aNajeriya Sheik Ibrahim Zakzaky da matar sa Malama Zeenat.

Babbar kotun jihar ce ta bayar da umarnin sakin malamin bayan da gwamnatin jihar ta gabatar da zargi takwas da ake yi a kan sa da matar sa.

Kotun ta wanke malamin da matar sa bayan da ta ce babu wata hujja da za ta ci gaba da sauraron ƙarar.

A cewar kotun, an gabatar mata da ƙarar Malam Zakzaky da matar sa a kan zargin tayar da fitina da sauran ƙunshin tuhuma, sai dai ta ce babu yadda za a yi a zargin mutum da aikata laifi a shekarar 2015 sannan a nemi hukunta shi a sabuwar dokar da aka samar a shekarar 2017.

Tunbi a ka mayar da Malam Zakzaky da matar sa zuwa gida bayan tsare shi da aka yi sama da shekaru huɗu.

An yi zaman shari’ar ne a jiya Laraba sannan jami’an tsaro sun bi umarnin kotu na sakin sa.

A baya kotu ta taɓa bayar da umarnin sakin shugaban shi’a amma a ka ƙi sakin sa su ka ci gaba da tsare shi.

A bangaren gwamnatin ta ce za ta ɗaukaka ƙara a bisa tuhumar da ta ke yi wa shugaban shi’a heik Ibrahim Zakzaky da mtar sa malama Zeenat.

Leave a Reply

%d bloggers like this: