Hukumar zaɓe mai zaman kan ta a Najeriya INEC ta sanar da ranar da za ta rufe rijistar katin zabe.

Shugaban hukumar ya ayyana ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2022 don dakatar da yin rijistar katin zaben da aka fara a ranar 29 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki.

Bayan dakatarwar hukumar za ta mayar da hankali ne don kammala aikin rijistar tare da miƙawa ga masu ita a don tunkarar zaɓen shekarar 2023.

Haka kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta gamsu da sabon tsarin da ta fito da shi na yin rijistar katin zaɓe a yanar gizo.

Shugaban hukumar a Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana hakan bayan ya jagoranci wasu mambobin hukumar zuwa wajen yin rijistar zaɓe a helkwatar hukumar zaben da ke Abuja.

Farfesa Yakubu y ace wannan ya isa misali, ganin yadda su ka tarar wajen babu Cunkoson jama’a.

Hukumar ta ce ta fito da sabon tsarin ne domin rage cunkuson jama’a a wuraren yin rijistar zaɓen da aka tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: