Wasu daga cikin iyalan marigayi Malam Nasiru Kabara sun buƙaci shugaba Buhariya sanya baki don sakin Malam Abduljabbar.

A wata doguwar watsiƙa da su ka aikewa shugaba Buhari wadda ke ɗauke da sunayen ƴaƴan Marigayi Malam Nasiru Kabara guda 19.

Wasiƙar ta musanta zargin da ake yi a kan ɗan uwan su Malam Abduljabbar Kabara, tare da tabbatar da cewar su ne na farko da za su fara sukar lamarin da an same shi da laifin.

Su ka ƙara da cewa, zargin da ake yi akan ɗan uwan su sharri ne sannan babu wata hujja da ke nuna ɗan uwansu yay i ɓatanci ga annabi.

Ƴan uwan nasu sun yi zargin an shirya wata muzgunawa da ɓatanci ga ɗan uwansu a don haka su ka buƙaci shugaban ƙasa ya saka baki don sakin ɗan usansu.

Haka kuma sun yi zargin malaman sun sauya wa’azuzzukan Malam Abduljabbar.

Wasiƙar da su ka kira da sunan ƙorafi wadda su ka gabatarwa da shugaban ƙasa sun ce zargin da ake yi a kan sa rashin adalci ne.

Dga cikin ƴaƴan marigayi Malam Nasiru Kabara 19 da su ka gabatar da wasiƙar ƙorafin akwai mata guda 14 sai maza guda biyar amma a cikin su babu khalifan dariƙar ƙadiriyya Ƙaribullah Nasiru Kabara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: