Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da samun masu ɗauke da nau’in cutar Korona samfurin Delta a ƙasar.

A daidai lokacin da ake samun ƙaruwar masu ɗauke da cutar Korona, gwamnatin ta ce an samu ɓullar nau’in Korona samfurin Delta.
Shugaban hukumar yaƙi da cutuka masu yaduwa a Najeriya Dakta Chikwe Ihekweazu ne ya tabbatar da haka yayin da yak e yi wa kwamitin yaƙi da cutar wanda fadar shugaban ƙasa ta kafa a Abuja.

Ya ce an samu nau’in cutar a jihohin Legas, Oyo da jihar Cros River sai babban birnin tarayya Abuja.

Gwamnatin ta ce an gano mutane 32 masu ɗauke da cutar a fadin ƙasar.
Sai dai hukumomi na cikin damuwa bisa yadda cutar ke yaɗuwa a cikin ƙanƙanin lokaci tare da halaka mutane da dama.
Nau’in cutar Korona samfurin Delta ya ɗaga hankalin hukumomin lafiya a duniya ganin yadda cutar ke da ƙarfi tare da saurin halaka jama’a.