Wata babbar kotun jihar Oyo ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same shi da aikata fashi da makami.

An yanke wa Ekemini Otuakak Edet hukuncin ne bayan ya aikata fashi a wani wajen siyar da magunguna a watan Maris din shekarar 2020.

Alƙalin kotun Okon Okon yay a bayar da umarnin rataye matashin mai shekaru 21 har sai ya mutu.

Alƙalin ya yanke hukuncin ne ƙarƙashin sashe na 1 (2a) na kundin doka wanda aka yi a shekarar 2004.

Hukuncin ya biyo bayan tabbatar da hannun wanda ake zargi da aikata fashi da makami a jihar.

Matashin mai shekaru 21 a duniya, mazaunin unguwar Oruko, a ƙaramar hukumar Orruefon Oruko ta jihar.

Sannan ya aikata fashin a wajen siyar da magunguna na MI AMAN da ke jihar Oyo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: