Gwamnatin Najeriya ta dauki aniyar dakatar da albashin likitocin da su ka tsunduma yajin aiki a fadin ƙasar.

Hakan ya biyo bayan rashin cimma matsaya da su ka yi bayan gwamnatin ta nemi zama da ƙungiyar likitocin masu neman kwarewa.

Gwamnatin ta bayar da umarni ga manyan likitoci a asibitocin koyar wa da su buɗe kundin rijista da zai ɗauki bayanan likitocin da ke yajin aiki a ƙasar.

Sannan dokar ba aiki ba albashi za ta fara aiki daga gobe Talata a kan duk wand aba ya zuwa aiki a ƙasar.

Sai dai ƙungiyar ta ce ba ta razana da barazanar da gwamnatin key i ba domin babu yadda za a yi gwamnati ta iya maye gurbin likitoci 16,000 da sabbi.

Ƙungiyar ta tsunduma yajin aikin ne bayan da a ka cika sama da kwanaki 100 ba tare da an cika musu alƙawuran su ba duk da cewar an yi zaman tattaunawar tsakanin bangaren biyu a baya.

Ƙungiyar ta buƙaci a biya su wasu haƙƙoƙin su da gwamnatin ta alƙawarta za ta ba su tun a baya.

Sannan sun shiga yajin aikin ne dalilin rashin mutunta yarjejeniyar da su ka yin a biya musu buƙatun su da su ka bayyana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: