Hukumar daƙile cutuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta ce sama da mutane dubu talatin ne su ka kamu da cutar amai da gudawa  a ƙasar.

Hukumar ta ce an samu ɓullar cutar ne a jihohi 22 na ƙasar.

A sanadiyyar cutar, an samu mutuwar sama da mutane 800 a jihohi daban daban na ƙasar ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Ƙididdigar da su ka yi ta fara ne daga watan Janairu zuwa watan Agustan shekarar da mu ke ciki.

Mafi yawa daga jihohin da cutar ta fi yaduwa a arewacin ƙasar ne kuma ciki har da jihar Kano.

Sai dai wasu masana na danganta hakan da yanayin ambaliyar ruwan sama da ake samu a daminar bana.

Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da cutar ta fi ta’azzara cikin jihohin Najeriya.

Cutar amai da gudawa na ƙara yaduwa a sassa daban-daban na ƙasar nan, a daidai lokacin cutar Korona ke yaduwa a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: